Mabuɗin Ilimi

Categories
    • faɗakarwa 1
    • Tarihi 3
Dark
Contact Us
ProfilMain Page
  • About us
  • Sponsored
  • Disclaimer
  • Privacy Policy

Recent posts

Views Style:
Dark
Muhadara- Dr. Isa  Ali Fantami

Muhadara- Dr. Isa Ali Fantami

No comments
Muhadara- Sheikh  Bin Uthman Kano

Muhadara- Sheikh Bin Uthman Kano

No comments
MUHADARA- SHEIKH AHMAD TIJJANI YUSUF GURUNTUM

MUHADARA- SHEIKH AHMAD TIJJANI YUSUF GURUNTUM

No comments
Yan'uwantaka A Musulunci

Yan'uwantaka A Musulunci

faɗakarwa No comments
Tarihin Sheikh Albani Zaria

Tarihin Sheikh Albani Zaria

Tarihi No comments
Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Tarihi No comments
Tarihin  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Tarihin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Tarihi No comments

Trending Post

  • Tarihin  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
    Tarihin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
  • Yan'uwantaka A Musulunci
    Yan'uwantaka A Musulunci
  • Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
    Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
  • Tarihin Sheikh Albani Zaria
    Tarihin Sheikh Albani Zaria
Email Subscription

Muhadara- Dr. Isa Ali Fantami

Oleh Osama Elguduwis - October 09, 2018



Cigaba da karatu »
  • Get link
  • Facebook
  • X
  • Pinterest
  • Email
  • Other Apps
Post a Comment

Muhadara- Sheikh Bin Uthman Kano

Oleh Osama Elguduwis - October 09, 2018


Cigaba da karatu »
  • Get link
  • Facebook
  • X
  • Pinterest
  • Email
  • Other Apps
Post a Comment

MUHADARA- SHEIKH AHMAD TIJJANI YUSUF GURUNTUM

Oleh Osama Elguduwis - October 09, 2018


Cigaba da karatu »
  • Get link
  • Facebook
  • X
  • Pinterest
  • Email
  • Other Apps
Post a Comment

Yan'uwantaka A Musulunci

Oleh Osama Elguduwis - March 18, 2018

yan’ Uwantaka a wajen malamai: itace tarayyar wani mutum da wani wurin haihuwa ko shayarwa,  amma ana iya aron Kalmar don amfani da ita ga dukkan abokin tarayya a qabila ko addini ko sana’a ko wata mu’amala ta soyayya ko wanin ta” ( Mufradat Arragib:7/317)

Ibn Hajar Al- asqalaaniy Yayi bayani game da fadin Allah: “Lallai Muminai Yan’ Uwan Juna ne” yace: “abun nufi wajen son junan su zuwa ga gamammen kira”. ( Fathul Baariy: 7/317).

Imamul Manaawiy yace: “Dan’ Uwa: shine wanda ya bubbugo tare da dan’ Uwan sa daga mabubbuga daya ta kowace fuska” (Attauqeef Alaa Muhimmaat Atta’areef,p:4)

Haka Imamaul Kafawiy ya nuna a cikin littafin sa Alkulliyaat shafi na sittin da uku.

FALALAR YAN’UWANTAKA
Yan’Uwantaka tana da falala mai yawa, daga ciki akwai:
karfafa ginshikin Musulunci: Son Dan’ uwa ga Dan’ Uwan sa yana daga mafi karfin ginshikin Musulunci, Abdullahi bin Abbas yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah sun Tabbata a gare shi yace: “ mafi karfin ginshikin Musulunci shine jibantar al’amura don Allah, da kiyayya don Allah, da so don Allah da fushi don Allah” ( silsilatul Ahaadith As- swaheehah, imamul Albaniy: 992. Sharhhus Sunnah, Imamul Bagawiy:3468. Addabraaniy: 125.)
Allah yana son wadanda sukai soyayya don shi: Abdullahi bin Abbas yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah sun Tabbata a gare shi yace: “Allah – mai girma da daukaka – yace: soyayya ta ta tabbata ga wadanda suka yi soyayya don ni ”( Imamu Ahmad:233, 247, Albaaniy fi Swaheehil Jaami’I 4331)
Yan’ Uwantaka na dandanawa mai yin ta zaqin Imani: Abu Hurairah yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata a gare shi yace: “wanda yake son ya sami zakin Imani sai yaso wani ba tare da wani dalili ba sai don Allah mai girma da daukaka” ( Swaheehul Jaami’i: 6164)
Zama akan karagu na zinari ranar Alqiyama: Abdullahi bin Abbas yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata A gare shi yace: “ Allah mai girma da daukaka yace: masu soyayya don ni suna da karagu na haske wanda har Annabawa da shahidai suna burin samun sa” (Swaheehul Jami’i: 4312)
Mafi girman daraja a wurin Allah wanda yafi son dan’ Uwansa: Ibnu Amr yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata A gare shi yace: “ mafi alhairin Abokai a wurin Allah mafi Alhairin su a tsakanin su” (Swaheehul Jami’i: 3270)
Soyayya don Allah na daga cikin Imani: Abu Hurairah yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata a gare shi yace: “ ba zaku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, ba zaku yi Imani ba har sai kuna son junan ku, shin kuna son in yi muku nuni da abun da idan kuka aikata shi zaku so junan ku? Ku yada sallama tsakanin ku” ( Muslim:54)
Mutum ranar qiyama ana ta da shi da wanda yake so: An samo Hadisi daga Anas dan Malik, lallai wani Mutum ya tambayi Manzon Allah akan tashin Qiyama, sai Manzon tsira da Aminci yace masa me ka tattala mata? Sai yace: babu komai sai dai ni ina son Allah da Manzon sa, sai Manzon Allah yace Masa: “ kai kana tare da wanda kake so”
Anas yace: ba muyi farin ciki ba, fiye da fadin Manzon Allah kai kana tare da wanda ka keso, Anas yace: ni ina son Manzon Allah da Abubakar da Umar, kuma ina fatan in kasance tare da su duk da ban yi aiki irin nasu ba..
LADUBBAN YAN’UWANTAKA
Ladubban Yan’uwantaka suna da yawa, wanda suka hada da:
Yin Yan’uwantaka don Allah kawai: Yan’Uwantaka don Allah tana kasancewa karbabba a wajen Allah matukar ba anyi ta don tunanin wata fa’ida ta duniya ba, sai dai kawai an yi ta don Allah ne. Manzon Allah (S.A.W) yace: “duk wanda yake son ya dandani zaqin Imani to yaso Mutum, soyayya don Allah kawai”
Zabar Abokin zama: lallai ne zaben Aboki yana da girman gaske a cikn Addinin Islama, domin ba kowane mutun ake Abota dashi ba, Manzon Allah (S.A.W) yace a Hadisin Abu Huraira “ lallai mutum yana kan Addinin Abokin sa don haka dayan ku ya duba wa zai yi abota da shi” ( Imam Ahmad: 7212, Abu daud: 4833, tirmidhi: 2387, Albaniy fes- swaheehah:927)
Kuma Manzon tsira yace: “kada kai abota da kowa sai Mumini kuma kada kowa ya shiga gidan ka sai mai tsoron Allah” ( Imamn Ahmad:3/380, Imam tirmidhi:2395, Albaniy swaheehul Jaami’i:7341)
Malamai sun ce lallai wanda za kai abota dashi ya cika siffofi biyar kamar haka:                               1. Ya zama mai hankali ba mahaukaci ba:wajibi ne  wanda zai zama abokin ka ya zama mai hankali, ba mahaukaci ba, ba fasiki ko wawa ba, domin fasiki ya yi kama da macijiya wadda ba’a samun komai a tare da ita sai cizo ko dafi. (Raudatul Uqala’i)

2.ya zama mai kyawawan dabi’u: Ibn Hibban yana cewa: lallai mai hankali kada yayi abota da kowa sai mai kyakkyawan ra’ayi, mai Ilimi da Addini, domin hakan yana nuna kai mai hankali ne. akwai wani tsohon Karin Magana da ke cewa “gaya mun abokin ka sai in gane kai waye (show me your friend and I will tell you who you are)”

3.kada ya zama mai son duniya:
Allah ta’ala yana cewa: “ ka kau da kai daga wanda ya juya baya daga ambaton mu bai nufin komai sai rayuwar duniya” Suratun Najmi: 29

Mai kwadayin duniya bai taimaka maka da komai sai halaka da tabewa ta hanyar sai da addinin ka don wani dan burin duniya wanda zai kare.

4.kada aboki ya zama mai bayyana fasikanci ba tareda kunya iko.

HAKKOKIN DAN ‘UWA
*Nuna wa Dan ‘uwa damuwa ya yin shiga kowane hali a rayuwa kamar yin tarayya da shi yayin farin ciki da yayin bakin ciki.
*Taimakon sa da dukiya, wannan yana kan matakai uku kamar:
taimaka masa da abun da yai saura na bukatun ka don ka share masa hawayen sa, kuma baka bukatar sai ya roke ka.
*Ajiye shi daidai da kai yayin bukata, kamar yadda kake wa kan ka haka kake masa komai, baka fifita kan ka akan sa.
*fifita shi akan ka yayin bukata, kamar yadda sahabbai suke yi
Taimakon sa wajen basa bashi yayin bukata, ko ka biya masa bashin da ya kasa biya, Abu Busrin ya ruwaito daga Manzon tsira cewa: “wanda ya taimaki wanda ke cikin qunci ko ya biya masa bashin sa, Allah zai saka shi a inuwar sa ranar da babu wata inuwa sai inuwar sa”.
*Gaishe shi yayin rashin lafiya, Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “duk wanda ya gaida mara lafiya ba zai gushe ba yana kan tafarkin Aljanna ko fiffiken ta”( Muslim: 2568
*Tsare masa sirrin sa, Jabeer dan Abdullah ya ruwaito daga Manzon tsira yana cewa: “Idan mutum ya baiwa dan uwan sa wani labari sannan ya juya baya, to – labarin- ya zama Amana” Abu daud: 4868).
Cika alkawarin sa, yana daga siffar muminai suna cika alkawari idan sun kulla kamar yadda Allah ya bayyana a cikin suratul Baqara, domin yana daga alamar munafunci kin cika alkawari kamar yadda manzon Allah yake cewa: “yana daga Alamar munafiki guda uku: idan yazo bada labari sai yai karya, idan yai Alkawari ya saba, idan an amince masa yai yaudara”
Karbar Uzurin sa da yarda da abun ya fadi
Yin nasiha ga Aboki yayin bukatar hakan, domin manzon Allah yana cewa: “hakkin muslmi akan musulmi shida ne”:
Idan ya hadu dashi yai masa sallama
Idan ya gayyace shi ya amsa masa
Idan ya bukaci addu’ar sa yai masa
Idan yai atishawa yai masa Addu’a
Idan yai ciwo ya gaishe shi
Idan ya rasu ya bi gawar sa
Yin nasiha a boye ba da niyyar tozarci ba
Kare shi daga suka ko batanci ko halaka gwargwadon iko.
HANYOYIN KARFAFA YAN’UWANTAKAR ISLAMA
Lallai Addini ya baiwa yan’uwantaka kulawa ta musamman inda ya sanya hanyoyin kyautatuwar ta da dama, kadan daga ciki sun hada da:

1.Yada sallama: lallai yana daga abun da ke karfafa yan’uwantakar Islama, ya kara son juna, yaada sallamar Islama tsakanin musulmai, kamar yadda yazo cikin Hadisin Abu Huraira (R.A) Manzo Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “ba zaku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za kuyi Imani ba har sai kuna son junan ku, shin ba nayi muku nuni ga wani abu ba wanda idan kuka aikata shi za ku so junan ku? Ku yada sallama a tsakanin ku” (muslim:54)

Musafaha: lallai yin musafaha da juna tana haifar da dankon soyayya tsakanin yan’uwa, bayan abun da ke cikin ta na lada mai girman gaske, kamar yadda a hadisin Barra’u dan Azib yace Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yace: “babu wasu Musulmai guda biyu da zasu hadu da juna suyi musafaha face an gafarta musu kafin su rabu da juna” ( Abu Dawua:5212, tirmidhi:2727, Albaniy fe swaheehil jaami’i:5777
Nuna soyayya da tausayawa juna: don fadin Manzon Allah (S.A.W): “misalin Muminai wajen soyayyar su da tausayin junan su da tausasawar su, kamar misalin jiki ne, idan wata gaba tai ciwo daga gare shi dukkan sauran jikin sai gume da zazzabi da rashin barci” (Bukhariy:6011, Muslim:2086)
Yiwa juna kyauta
Yin hakan yana da tasiri mai girma a musulunci, kuma yana haifar da kauna da soyayya tsakanin masoya

Fada masa kaunar sa: Bada labarai ga wanda kake so cewa kana son sa, domin hakan yana daga cikin sunnah
Nuna kan kan da kai ga juna: ba tareda nuna girman kai ko fifiko ga juna ba
Yawan ziyartar juna: domin mai ziyara hatta mala’iku suna neman masa gafara, kuma yana kan tafarkin Aljannah har ya dawo
CIKASAWA:
lallai Yan uwantakar Islama girman matsayin ta ya wuce dukkan wata Yan’ uwantaka a duniya, domin tana dauke da tausasawa, tausayawa, yafiya, taimakon juna, sannan kuma kare mutunci, dukiya da jinin juna daga dukkan sharri.

Don haka wajibi ne a gare mu mu zama masu bin karantarwar Islama don neman tsira duniya da lahira.

Allah muke roko ya karfafa yan’uwantakar mu akan abunda yake so kuma ya yarda da shi.

Wal hamdu lillaahi rabbil Aaalameena
Cigaba da karatu »
  • Get link
  • Facebook
  • X
  • Pinterest
  • Email
  • Other Apps
Post a Comment
Nhãn : faɗakarwa

Tarihin Sheikh Albani Zaria

Oleh Osama Elguduwis - March 18, 2018

An haifi Ash-Sheikh Albani Zaria ne a watan Rabiu Thani 1379 dai dai da 27 Sept 1960, a cikin garin Muciya Zaria, Sabon Garin Kaduna, Najeriya.
  Malam ya taso tun yana yaro da son ilimi kamar yadda wani malamin shi ya siffanta shi da cewa: “Albaniy tun yana 'Karami da angan shi ina kaje; karatu, ina zaka; karatu, me kake yi; karatu, me ka gama; karatu.
   Mahaifiyar shi mai Suna Saudatu ita ta fara bashi 'karfin guiwar karatun addini na musamman, domin itace wadda ta fara siyar da akuyar ta, ta bashi kudin ya siyo littafin Saheehu Muslim inshi na farko. Har ila yau mahaifiyarshi ta taba 'daukan shi tun yana 'karami ta kaishi gurin wasu malamai a cikin garin Kano domin su karantar dashi Karatun addini da zummar cewa 'danta ya zama Malami.
     A 'bangaren karatun Al-Qur'ani; Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara karatun Allo ne a cikin anguwar mucciya dake Zaria. A inda ya sauke Qur'ani saukar Farko ruwayar warsh 'kira'ar Nafi'u a hannun Mallam Mato da Alarama Mallam Abubakar.
  A 'bangaren Larabci kuwa Ash-Sheikh Albani Zaria ya halarci wani karatu na wata goma sha takwas (18 months) a 'karkashin wani tsarin karatu da marigayi Gaddafi ya kawo Nigeria, a 'karkashin Jagorancin jami'ar Libiya a shekara alif dubu 'daya da 'dari tara da tasa'in. Babban Malami, marigayi Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, shi ya danka musu takardar shedar kammala karatun, kuma sai da yaba Albani Zaria wata takarda na jinjinawa ta musamman.
  Dangane da sauran karatuttukan addinin musulunci kuma. Ash-Sheikh Albani Zaria yayi karatu a hannun Malamai da dama anan gida Nigeria da kuma Saudiya.
  Kadan daga cikin malaman da yayi karatu a hannun su anan gida Nigeria sun kasance kamar haka; Dr Aminuddeen Abubakar Kano (Mai makarantar Kwali), Ash-Sheikh Sani Yakubu Zaria, Shehu Umar (Malami ne a Jami'a), Alkali Mallam Haruna Ishaq Zaria. Daga bisani Ash-Sheikh Albani Zaria (Rahimahullah) ya tare a hannun wani mutumin india mai suna Dr AbdulRahim Muhammad Muslim Khan wanda malami ne dake koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Mallam Muhammad Muslim Khan ya karantar da Albani Zaria littattafai masu yawa. A bangaren ilimin hadisi wannan malami Muhammad Muslim Khan ya karantar da Ash-Sheikh Albani Zaria littafin tadriburra'wi da musdala'ul hadith. A bangaren sauran littattafai kuma wannan malami ya karantar da Albani littafin Sifatu-Salatin Nabiy da kuma littafin Sharhus- Sunnah na Alhafiz Al-Bagawiy.
   Daga baya a lokacin da Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara kasuwanci yana samun kudi, malam ya kasance yakan sayi tiket na jirgi musamman dan yaje 'Kasar Saudiyya yayi karatu a matsayin shi na 'dalibi mai niman ilimi bawai a matsayinshi na 'dalibin jamiatul Islamiyya ba.
   Mallam yayi karatu a gaban Dr Muhammad Amin dake jamiatul Islamiyya dake madina, a inda ya koyi 'kira'ar Qur'ani 'kira'a bakwai ruwaya goma sha hudu.
   Mallam Ya yi karatu a gaban Sheikh Uthaimin karatu sosai musamman ta fannin ilimin tafseerin Al-Qur'ani mai girma.
   Mallam yayi karatun Aqeeda karatu sosai a hannun Addoktur Assuhaimi da professor Ali Nasir Faqihi wadanda dukkaninsu malamai ne a jamiatul islamiyya dake madina Kulliyatud-Da'awa wa usuluddeen.

Mallam yayi karatu a wurin mallam Tuwaijiri wanda ke karantarwa a Daruul-Hadeethisil Khairiyya dake Saudiyya.

Mallam yayi karatu a wajen Sheikh Zarban Al-gamidy, wanda shi ne tsohon Bursar (shugaban 'bangaren kudi) a jami’ar Madina.

Mallam yayi karatu a hannun Sheikh Abdullahi Bn AbdulRahman Alu Bassam (mai littafin taysirul Allam).

Mallam yayi Karatu a gaban Professor Samir wanda 'dalibi ne na Sheikh Nasiruddeen Albani.

Mallam yayi karatu a hannun Muhammad ibn Ali ibn Adam Al Ethiopy wanda shi kuma mutumin 'kasar Ethiopia ne.

Akwai malaman jami’ar Madina da yawa wadanda malam yayi karatu a gaban su, amma ba’a matsayin shi na 'dalibi a jami’a ba, A’a, a matsayin shi na 'dalibi wanda ya kai kanshi koyon ilimi a wurin su.

Allah ya jikansa ya gafarta masa yasa ya huta. Ameen.
Wassalamu Alaikum
Cigaba da karatu »
  • Get link
  • Facebook
  • X
  • Pinterest
  • Email
  • Other Apps
Post a Comment
Nhãn : Tarihi

Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Oleh Osama Elguduwis - March 17, 2018
 

An haifi marigayi Sheikh
Ja'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacinyakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da
Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar
Nijar ne,amma yake zaune aunguwar Fagge a Kano. Tunkafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya rigaya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala ashekara ta 1978 Bayan da Malam ya kammala
haddar Alkur'ani mai girma, kasan cewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekarata 1980. Ya shiga makarantar
koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar
manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan
makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya
kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta
Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri
na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan.
Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir
(PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar,Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago,wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja,
wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin
limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano.Daga cikin malamansa na jami'a
kuma, akwai Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt. Daga cikin karatut -tukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai
girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfus -shubuhaat, Bulugul Maraam,Riyaadus- salihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy.
Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi'u Umar R/Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Malam Abdullah Usman Gadon Kaya da Malam Usman Sani Haruna da Malam Ibrahim Abdullahi Sani da Malam Ali Yunus Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu
Hamisu Kura da Malam Anas Muhammad Madabo. Kafin rasuwarsa ya fara gagarumin aikin rubuce
tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre) marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi.
Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai rasuwarsa.
an binne shi ne a makabartar Dorayi.


Allah madaukakin sarki Ya jikansa ya gafarta masa yasa ya huta
Ameen.
Wassalamu Alaikum
Cigaba da karatu »
  • Get link
  • Facebook
  • X
  • Pinterest
  • Email
  • Other Apps
Post a Comment
Nhãn : Tarihi

Tarihin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Oleh Osama Elguduwis - March 17, 2018

sheikh brahim bin Muhammad bin Bilal. Mahaifinsa
shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-
Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da
tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,
bayan  da sana’ar dinki, domin dogaro da kai. Sunan mahaifiyarsa Hajiya Sa’adatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
An haife shi a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32
unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala ya fara karatun Alqur’ani mai girma tun yana dan
karami, kuma ya haddace shi a lokacin yana  da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da
Ya yi ya kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan
mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi
da fannoninsa daban-daban. Wadannan manyan malamai su ne:
Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda yayi karatun Alqur’ani a wajensa, Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda ya yi karatun Alqur’ani a wajensa, Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda ya yi karatun Alqur’ani a wajensa, Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja, Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda ya yi gyaran tilawa a wajensa, Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda ya yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa, Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda ya yi lugga da fiqihu da tafsir a wajensa, Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda ya yi hadith da lugga a wajensa, Sheikh Zakari Mai littafi, wanda ya yi lugga da fiqihu a wajensa, Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda ya yi nahawu da fiqihu a wajensa, Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda ya yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a
wajensa ya yi tsawon shekara ashirin yana karatun ilimi a wajensa, Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda ya yi fiqihu da lugga a wajensa, a wajensa ya sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai
haquri da juriyar karantarwa, Dr. Kabiru M. K. Yunus BUK, wanda ya yi nahwu da lugga a wajensa, Dr. Aminuddeen Abubakar, shugaban Da’awah, wanda ya yi tauhidi da hadith a wajensa, Dr. Ahmad Bamba BUK, wanda ya yi hadith a wajensa, Dr. Abubakar Jibirin, wanda ya yi Kitabut Tauhid a wajensa,  Sheikh Abdulwahab Abdallah, wanda ya yi Musdalahul Hadith, da Qadarunnadah (nahawu), da
Subulussalam (hadith) a wajensa.
Wadannan su ne malaman da ya kwashe mafi yawan shekaruna yana zirga-zirga a tsakaninsu, wajen
neman ilimi. Akwai wasu malaman da suka yi mishi tasiri a rayuwa, amma ta hanyar karanta
littattafansu da sauraren kaset-kaset dinsu:
1. Sheikh Muhammad bin Saleh Usaimin. Wannan malamin ne ya kwashe tsawon shekara goma yana bin littattafansa da kaset-kaset dinsa na audio da bidiyo
2. Almuhaddith Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani. Wannan malami, duk littattafansa da suka
fito kasuwa, da kaset-kaset, yana bibiyar su, saboda fa’idoji masu yawa.
3. Sheikh Bakar Abu Zaid. Saboda kwarewarsa a wajen sarrafa littattafai.
Sauran su ne, Sheikhul Islam Ibni Taimiyya, da Sheikh Ibnul Qayyim, da Sheikhul Islam Azzahabiyy,
da Sheikhul Islam Ibni Kathir, da Sheikhul Islam Ibni Hajar Al-Asqalani.
Aqidar sa ita ce aqidar ahlussunnah wal jama’a. Ma’ana, imani da Alqur’ani da hadisan Manzon
Allah (SAW) a kan fahimtar magabata na kwarai.
Tsarin wa’azi: Tsakatsaki.
Ya ci gaba da karatu na zamani a Jami'ar Bayero, a bangaren jarida, Mass Comm. Wasu dalilai suka
tsayar da shi. Ya yi diploma a computer data processing.
Iyali: A yanzu yana da mata biyu, da kuma ‘ya’ya tara.
Daga cikin kasashen da ya je domin wa’azantarwa, akwai Nijar, Togo da sauransu.
Allah ya taimakeshi ya Kara bunkasa masa iliminsa Ameen
Wassalamu Alaikum warahmatulla
Cigaba da karatu »
  • Get link
  • Facebook
  • X
  • Pinterest
  • Email
  • Other Apps
Post a Comment
Nhãn : Tarihi
Subscribe to: Posts (Atom)
Powered by Blogger


Copyright © 2015 - 2017 Blog Indoor | Designed with by
Fancybloggertricks
About Us | Sitemap | Hire Us | Privacy & Policy | Advertise | Sitemap | Write For Us | Sponsor A Post | Own A Site | Disclaimer

SEARCH BLOGINDOOR

SUBSCRIBE TO OUR POST

Subscribe With Us!
Why should I subscribe?
  • ✔
    For Latest Free Browsing Tweaks
  • ✔
    Android & PC Tutorials
  • ✔
    Tech News & HOW TOs
  • ✔
    All Straight into your → INBOX
Safe With Us | Privacy Policy

Pages

  • Home

⚠ WARNING: Ba Mu Da Hakkin Tallan da ake gani a wannan Site din.


Home | About us | privacy-policy | contact us | Sponsored Post
Disclaimer

© Copyright 2021" Osama Elguduwis · All Rights Reserved · And Our Sitemap · All Logos and Trademark Belongs To Their Respective Owners·