Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

 

An haifi marigayi Sheikh
Ja'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacinyakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da
Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar
Nijar ne,amma yake zaune aunguwar Fagge a Kano. Tunkafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya rigaya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala ashekara ta 1978 Bayan da Malam ya kammala
haddar Alkur'ani mai girma, kasan cewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekarata 1980. Ya shiga makarantar
koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar
manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan
makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya
kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta
Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri
na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan.
Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir
(PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar,Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago,wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja,
wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin
limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano.Daga cikin malamansa na jami'a
kuma, akwai Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt. Daga cikin karatut -tukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai
girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfus -shubuhaat, Bulugul Maraam,Riyaadus- salihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy.
Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi'u Umar R/Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Malam Abdullah Usman Gadon Kaya da Malam Usman Sani Haruna da Malam Ibrahim Abdullahi Sani da Malam Ali Yunus Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu
Hamisu Kura da Malam Anas Muhammad Madabo. Kafin rasuwarsa ya fara gagarumin aikin rubuce
tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre) marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi.
Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai rasuwarsa.
an binne shi ne a makabartar Dorayi.


Allah madaukakin sarki Ya jikansa ya gafarta masa yasa ya huta
Ameen.
Wassalamu Alaikum
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://mabudinilimi.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts