Tarihin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa


sheikh brahim bin Muhammad bin Bilal. Mahaifinsa
shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-
Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da
tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,
bayan  da sana’ar dinki, domin dogaro da kai. Sunan mahaifiyarsa Hajiya Sa’adatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
An haife shi a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32
unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala ya fara karatun Alqur’ani mai girma tun yana dan
karami, kuma ya haddace shi a lokacin yana  da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da
Ya yi ya kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan
mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi
da fannoninsa daban-daban. Wadannan manyan malamai su ne:
Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda yayi karatun Alqur’ani a wajensa, Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda ya yi karatun Alqur’ani a wajensa, Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda ya yi karatun Alqur’ani a wajensa, Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja, Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda ya yi gyaran tilawa a wajensa, Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda ya yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa, Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda ya yi lugga da fiqihu da tafsir a wajensa, Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda ya yi hadith da lugga a wajensa, Sheikh Zakari Mai littafi, wanda ya yi lugga da fiqihu a wajensa, Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda ya yi nahawu da fiqihu a wajensa, Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda ya yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a
wajensa ya yi tsawon shekara ashirin yana karatun ilimi a wajensa, Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda ya yi fiqihu da lugga a wajensa, a wajensa ya sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai
haquri da juriyar karantarwa, Dr. Kabiru M. K. Yunus BUK, wanda ya yi nahwu da lugga a wajensa, Dr. Aminuddeen Abubakar, shugaban Da’awah, wanda ya yi tauhidi da hadith a wajensa, Dr. Ahmad Bamba BUK, wanda ya yi hadith a wajensa, Dr. Abubakar Jibirin, wanda ya yi Kitabut Tauhid a wajensa,  Sheikh Abdulwahab Abdallah, wanda ya yi Musdalahul Hadith, da Qadarunnadah (nahawu), da
Subulussalam (hadith) a wajensa.
Wadannan su ne malaman da ya kwashe mafi yawan shekaruna yana zirga-zirga a tsakaninsu, wajen
neman ilimi. Akwai wasu malaman da suka yi mishi tasiri a rayuwa, amma ta hanyar karanta
littattafansu da sauraren kaset-kaset dinsu:
1. Sheikh Muhammad bin Saleh Usaimin. Wannan malamin ne ya kwashe tsawon shekara goma yana bin littattafansa da kaset-kaset dinsa na audio da bidiyo
2. Almuhaddith Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani. Wannan malami, duk littattafansa da suka
fito kasuwa, da kaset-kaset, yana bibiyar su, saboda fa’idoji masu yawa.
3. Sheikh Bakar Abu Zaid. Saboda kwarewarsa a wajen sarrafa littattafai.
Sauran su ne, Sheikhul Islam Ibni Taimiyya, da Sheikh Ibnul Qayyim, da Sheikhul Islam Azzahabiyy,
da Sheikhul Islam Ibni Kathir, da Sheikhul Islam Ibni Hajar Al-Asqalani.
Aqidar sa ita ce aqidar ahlussunnah wal jama’a. Ma’ana, imani da Alqur’ani da hadisan Manzon
Allah (SAW) a kan fahimtar magabata na kwarai.
Tsarin wa’azi: Tsakatsaki.
Ya ci gaba da karatu na zamani a Jami'ar Bayero, a bangaren jarida, Mass Comm. Wasu dalilai suka
tsayar da shi. Ya yi diploma a computer data processing.
Iyali: A yanzu yana da mata biyu, da kuma ‘ya’ya tara.
Daga cikin kasashen da ya je domin wa’azantarwa, akwai Nijar, Togo da sauransu.
Allah ya taimakeshi ya Kara bunkasa masa iliminsa Ameen
Wassalamu Alaikum warahmatulla
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://mabudinilimi.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts

More posts